Daga Rukayya Abdullahi Maida
Ma’aikatar Albarkatun ruwa ta jihar kano ta Barranta kanta da zargin da akeyi na wata Takarda dake yawo a social media da kafafen yada labarai cewa kwamishinan Maaikatar Hon. Gwani Ali Haruna Makoda, ya bada umarnin kwanto wani injin din ban ruwa dake mazabar karefa a Karamar Hukumar Tudun Wada anan Kano.
Daractan dake Kula da Bangaren Noman Rani da dama-damai na jihar Kano Adamu Chiroma Shi ne ya Sheda haka yayin ganawa da manema labarai yau Litinin a Ofishin sa.
Inda yace Sam kwamishina Bashi da masaniya Kan wannan Takarda da aka rubuta, wadda ke Nu na Shi ya bada Umarnin kwanto injin din don a kawo Shi jihar Kano daga Tudun Wada.

Ya Cigaba da cewa wasu yan tsirarin maaikata ne bisa Jagorancin Daractan Mulki na maaikatar, Abubakar Gambo Dana ban Ruwa, da wasu yara da suka hayo Ake zargi da aikata wannan Aika-aikar, an kuma ce har sun karbi wani Kaso na dubu Dari biyar tun kafin ciniki ya fada duk ba tare da sanin maaikatar ba.
Ku yi Murna Cikin kwanciyar hankali, Idan Kotun Ƙoli ta tabbatar da Gawuna – Rarara ga yan APCn Kano
Bugu da Kari an same su da hannu dumu-dumu wurin rubuta Takarda Kan cewa Shugaban Karamar Hukumar Hadi da DPO na Tudun Wada su Amince da kwanto injin din ban ruwan tunda umarnin Kwamishi ne.
To sai dai kafin su cimma gaci kwamishina ya samu rahoto ta hanyar Kiran waya, ya kuma binciki daractocin dake da ruwa da tsaki Kan duk wasu injina kafin shi Domin samun gaskiyar lamari, daga bisani ya Fuskanci babu masaniyarsu.
Matakin farko bayan binckiken da kwamishinan Albarkatun Ruwa Hon. Gwani Ali Haruna Makoda ya dauka bayan Tabbatar da Almundahana wadancen maaikata keson aikatawa, Shi ne ya umarcesu dasu rubuta Takardar da zata wankeshi daga bata masa suna da sukayi, kamar yadda suka rubuta tun da farko don bata Sunan shi, bayan jami’an yansanda naTudun Wada sun kamesu zuwa ofishinsu, donyin bincike kana kuma aka cafko sauran wadanda Ake zargi gaba daya aka mikasu ga shelikwatar Hukumar Yan sanda Dake Bampai anan Kano don ta Cigaba da bincike.