Daga Rukayya Abdullahi Maida
Babban Bankin Najeriya, CBN, ya sanar da bankuna da ‘yan Najeriya cewa su yi hattara da jabun takardun naira musamman kudaden da ake kashewa a wuraren sayar da abinci da sauran cibiyoyin kasuwanci a kasar.
A cewar Babban Bankin, laifi ne da za a iya yanke wa mutum hukuncin dauri a gidan yari idan aka kama shi da jabun takardun kuɗin.
Babban Bankin ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

CBN ya ci gaba da cewa, “An jawo hankalin CBN kan yadda wasu mutane ke yawo da jabun takardun kudi, a kasuwannin sayar da kayan abinci da cibiyoyin kasuwanci a manyan biranen kasar nan.“
Hukuncin Kotun Koli: ‘Yan sanda sun yi sabon gargadi ga al’ummar jihar Kano
Don kauce wa shakku, sashe na 20 (4) na dokar Babban Bankin (2007) da aka yi wa kwaskwarima, ya bayyana karara cewa amfani da jabun takardun kuɗi a hannun jama’a ko kasuwanni a Najeriya laifi ne da za a yanke hukuncin dauri mafi karanci na shekaru biyar.
“CBN na ci gaba da hada kai da hukumomin tsaro domin kwace irin waɗannan jabun takardun kudin Naira da kuma gurfanar da masu su a kotu.“
Haka kuma ana kira ga jama’a da su kai rahoton duk wanda ake zargi yana da jabun takardun naira zuwa ga hukumomi.