Zaɓen 2023: Ba za mu bari barazana akan mu ko Ra’ayin wasu ya yi tasiri wajen yake hukunci ba – Alkalin Alkalai

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

A karshe dai babban alkalin alkalan Najeriya, Olukayode Ariwoola, ya mayar da martani kan zarge-zargen nuna son kai a kan batutuwan da suka shafi Shari’un zaben 2023 a Nigeria.

Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa kotunan sauraren kararrakin zabe da kotun daukaka kara sun soke zabukan da aka yi na masu rike da mukaman gwamnati da aka zaba a matakai daban-daban a babban zaben da ya gabata.

Kotu ta kori wasu gwamnoni da Sanatoci da ‘yan Majalisar Wakilai saboda korafin da jam’iyyun adawa suka yi akan su.

Magoya bayan shugabannin da aka kora dai sun zargi bangaren shari’a da cewa suna yiwa jam’iyyar APC aiki ne.

Sai dai da yake magana a wajen bude zama na musamman na shekarar shari’a ta 2023/2024 da kuma rantsar da sabbin manyan lauyoyin Najeriya masu lambar kwarewa ta SAN 58, Ariwoola ya bukaci alkalai da su tsaya tsayin daka, yana mai cewa bai kamata a ruguza tunanin shari’a ba.

Ya roƙi alƙalai da kada su damu da abubuwan da‘ yan Siyasa suke yi akan su.

Ya ce, “Ya zama dole a yi la’akari da cewa ra’ayin jama’a, ba za su taba kasancewa a matsayin doka ba wajen yanke hukunci kan shari’o’in da ke gaban ku.

“Dokar za ta kasance doka, ko da kuwa abin da ya shafi kowa ne. A cikin duk abin da muke yi, a matsayinmu na masu fassarar doka, ya kamata mu yi ƙoƙari mu raba ra’ayi daga tunani da zato daga gaskiya.

“Bai kamata mu bari barazana ko zarge-zarge ko kwarmaton wasu su shafe mu ba, har mu zo mu fara dagula doka da kokarin farantawa wasu rai wajen yanke hukunci ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika sakon ta’aziyyar Rasuwar Aminu Dantata

Daga Sadiya Ahmad   Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika...