Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano Abba Kabir ya nada sabon shugaban ma’aikatan jihar

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

Gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nada Alhaji Abdullahi Musa a matsayin sabon shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24.

Yace nadin nasu na zuwa ne bayan da tsohon shugaban ma’aikatan jihar kano Usman Bala ya kammala aikin sa , Inda yayi ritaya daga aikin gwamnati tun a watan mayun shekara ta 2023, kamar yadda doka ta tanada .

Talla

Sanarwar ta ce Alhaji Abdullahi Musa kwararen ma’aikacin gwamnati ne da yayi aiki a hukumomi da ma’aikatun gwamnatin jihar kano, kuma haifaffen karamar hukumar Kiru ne.

Sabon Shugaban Ma’aikatan gwamnatin jihar kano Abdullahi Musa

Abdullahi Musa ya taba zama babban Sakatare a gidan gwamnatin jihar kano da majalisar zartarwa ta jihar da kuma ma’aikatar aiyuka na musamman da dai sauransu.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bukaci sabon shugaban ma’aikatan da ya gudanar da aikin sa cikin kwarewa da bin dokoki da ka’idojin aikin gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar ’Yan Jaridun Kano Arewa ta Aike da Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Alhaji Aminu Dantata

  Kungiyar ’Yan Jarida ta Kano Arewa ta bayyana alhinin...

Ku na da rawar takawa wajen inganta Lafiyar al’ummar Kano – Waiya ga jami’an yada labarai

Daga Abubakar Sayeed Kwamishinan Ma'aikatar yada labarai da harkokin cikin...

Ana daf da yin jana’izar Aminu Dantata a Madina

Tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa Madina na...