Rasuwar Darakta Aminu S Bono: Forodusa Abdul Amart na shan yabo

Date:

Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman

Kwanaki bakwai bayan rasuwar babban Darakta a masana’antar Kannywood Aminu S Bono, babban mai shirya fina-finan Abdul Amart ya sanyawa Iyalan mamacin gidan na Naira Miliyan 4, bayan ya gano cewa a gidan haya mamacin yake.

Wasu daga cikin dangin mamacin sun tabbatar da cewa Abdul Amart wanda ake yiwa lakabi da mai kwashewa ya sayawa Iyalan Aminu S Bono gida a unguwar Dandago na Naira Miliyan 4.

Wannan abun alkhairi da Abdul Amart yayi yasa al’umma da dama suke ta yaba masa bisa yadda ya nuna tausayi da zumunci don kyautata rayuwar abokin aikin sa bayan babu ransa.

Talla

Ga wani rubutu Auwal Muhammad Danlarabawa akan wannan bayi akan batun

Duk shaharar da Marigayi Darakta Aminu S Bono yayi a kannywood Bai mallaka gidan kansa ba, sai bayan Mutuwarsa Abdul Amart ya Saya masa Dan iyalansa su zauna a ciki.

Baya mutuwar Aminu S Bono sai ga wani kabaki na Arziki da ya samu iyalansa Ma’ana matar sa da Yayansa da suka kasance marayu a halin yanzu Wanda wani bawan Allah Daga industry din ya gwangwaje su da Abin arziki.

Abdul Amart shine Wanda ya bincika yaga cewar Ashe wannan bawan Allah a gidan haya yake zaune bashi da gida na kanshi Nan take aka Nemo gida aka Saya musu sannan aka danka wannan gida a hannun matarsa da yayan da ya bari Dan su samu muhallin zama.

Fasadin da ake yi a jami’o’i ba’a yin sa a Kannywood – Isma’il Muhammad

Wannan lamari yayi min Dadi sosai Wanda nasan halin da ake fadawa yayin da magidanci ya mutu yabar Yayansa da Matarsa a gidan haya cewar Amb Auwalu Muhd Danlarabawa.

Amb Auwalu Muhd Danlarabawa ya Yaba wa wannan producer Abdul Amart tare da Yi Masa addua ta musanman duba ga Yana da Gidauniyar Tallafawa Mabukata Daga Tushe wato Grassroot Care and Aid Foundation yasan halin da Marayu ke kasancewa da matan da aka bar musu Marayu a rayuwa.

Daga Nan Kuma Amb Auwalu Muhd Danlarabawa ya Kara yin Kira ga daukacin Daraktoci da jarumai dama masu shiryawa akan su Kara hada kawunansu wajen ganin sunci gaba da gudanar da ayyukan alkhairi irin wannan ga Marasa lafiya da iyalan da aka Mutu aka bari hakan zai taimaka sosai Kuma a samu lada.

Sannan yayi Kira ga daukacin al’umma da suke musu Kallo na daban da su fahimci cewar ita rayuwa a kowanne mataki ana samun na aleziki da akasin haka Kuna a haka zaa rayu har tashin alkiyama.

Yayi wannan Kira ne yau a wajen taron addu’a da aka gabatar ga mamata na kannywood wanda dama an saba yi a irin wannan lokaci a Jihar ta Kano karkashin Jagorancin dattawa da masu fada aji a masanaantar Baki Daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...

Da dumi-dumi: Wasu kungiyoyin APC a Kano sun fara kiraye-kirayen Abdullahi Abbas ya sauka daga shugaban jam’iyyar

Daga Hafsat Abdullahi Muhammad Kungiyoyin jam'iyyar APC da suka hadar...

Bayan Amincewar Kasar Saudia , an Sanya Ranar Binne Aminu Dantata a Madina

Babban sakataren marigayi Alhaji Aminu Dantata, Mustapha Abdullahi Junaid...

Rashin Alhaji Aminu Dantata Babban Rashi ne ga harkokin kasuwanci a Duniya – Salbas

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Babban kamfani a masana'antar mai a...