Hukumar Karota ta yi holin Muggan kwayoyi da kayan da wa’adin su ya kare

Date:

Daga Hafsat Lawan Sheka

 

Hukumar kula da zurga-zurgar ababen hawa ta Kano Karota ta yi holin miyagun kwayoyi na kimannin Miliyan 210 da katan din taliyar yara guda 100, Da allura da dai sauransu.

Kadaura24 ta rawaito Kakakin Hukumar Nabilisi Abubakar Kofar Na’isa ne ya bayyana hakan a wata ganawa dayayi da ‘yan jaridu a Helikwatar Hukumar a wannan rana.

Talla

Nabilisi yace cikin abinda Hukumar ta kama harda Magannin karfin maza, da allurar dake gusar da hankali, dama nau’ikan kayan kwalam da makulashe na yara.

A don haka shugaban hukumar ta karota Engr Faisal Muhmud Kabir yake kira ga al’umma wajen kula da abinda zasu saya ko na ci ko na sha domin tabbatar da cewar basu sayi kayan da wa’adinsu ya kare ba, don gudun fadawa barazana ga lafiyar yara dama al’umma baki daya.

Yace ko satin daya gabata sun sami labarin wani daya sha kwaya kuma daga karshe tayi ajalinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika sakon ta’aziyyar Rasuwar Aminu Dantata

Daga Sadiya Ahmad   Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika...