Daga Hafsat Yusuf Sulaiman
Rahotanni daga filin jirgin saman Abuja na cewa kungiyoyin kwadago sun rufe titin da ke zuwa filin jirgin saman da safiyar yau, Alhamis.
Da safiyar nan ne, mutane suka rika wallafa bidiyo na yadda motoci da masu ababen hawa suka tsaya jingum-jingum a kan titin. A daya daga cikin bidiyon da aka wallafa a shafin X, ana iya ganin wata motar dakon kaya daga nesa an gindaya ta a tsakiyar titi.

Haka zalika, an jiyo kade-kade na tashi, yayin da ake iya hango wasu mutane sanye da tufafi iri daya a kan motocin da ke nesa.
Sakataren tsare-tsare na kungiyar NLC, Kwamared Nasir Kabir ya shaida wa BBC cewa mambobinsu sun rufe titin shiga filin jirgin saman na Abuja da kuma hana duk wani jirgin sama da ke da niyyar tashi zuwa jihar Imo.
Dakile Harin Boko Haram a Kano: Sarkin Gaya ya Gargadi Hakimai, Dagatai da Masu Unguwanni
Haka kuma wata sanarwa da babban sakataren NLC, Kwamared Emmanuel Ugboaja ya fitar ta ce matakin ya hadar da filin jirgin sama na Lagos.
Ta kuma ambaci matakin da ‘yan kwadagon ke dauka a dambarwarsu da gwamnatin jihar Imo.
A ranar Laraba dai 8 ga watan Nuwamban 2023, kungiyoyin kwadago na NLC da TUC suka fara wani yajin aiki, wanda suka sanar da rufe duk wasu harkokin samar da lantarki da na sufurin jiragen sama a jihar ta Imo.
Matakin na zuwa ne kwanaki kalilan bayan zargin da kungiyar NLC ta yi wa gwamnan jihar Hope Uzodinma da hadin bakin ‘yan sanda wajen kama shi tare da dukan sa. ‘Yan kwadagon daga bisani sun nuna hoton shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero da idonsa na dama a kumbure.