Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Shugaban ƙasar Nigeria Bola Tinubu ya amince da nadin Muhammad Abba Isa a matsayin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin masu bukata ta musamman.
A cewar wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Alhamis, yace nadin na cikin kudirin Tinubu na tabbatar da cewa kowane bangare na al’umma ya samu isasshiyar dama a gwamnatin sa.

”Muhammad Abba Isa fitacce ne wanda ya kwashe sama da shekaru 10 yana bada shawarwarin yadda za’a inganta rayuwar Masu bukaci ta musamman a gida Nigeria da kasashen waje,” in ji sanarwar.
Yan kwadago sun rufe titin zuwa filin jirgin sama na Abuja
‘’Sabon mai taimaka wa shugaban kasa ya kammala karatunsa kan harkokin mulki a jami’ar Maiduguri, inda kuma yayi Digirin na biyu a wannan fannin a dai jami’ar ta Maiduguri a shekarar 2017.
Shugaban ya bukaci sabon mai bashi shawara da ya samar da hanyoyin da za a bi don shigar da masu bukata ta musamman cikin manufofi da shirye-shiryen dukkan ma’aikatu, sassan da hukumomin gwamnatin tarayya tare da yin aiki kafada da kafada da kananan hukumomi don aiwatar da shirin, don inganta rayuwar su.