Yanzu-Yanzu: Kotun koli ta Yanke Hukunci Kan Shari’ar da Atiku ya Kalubalanci Nasarar Tinubu

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

A ranar Alhamis din nan ne kotun kolin Nigeria ta tabbatar da nasarar da shugaba Bola Tinubu ya samu a zaben Shugaban kasa, wanda ya kawo karshen kalubalen shari’a da manyan abokan hamayyarsa biyu suka shigar, inda suka ce nasarar da ya samu ta samu ba halastacciya bace.

Hukuncin dai ya bai wa Tinubu mai kimanin shekaru 71 da haifuwa nasarar cigaba da shugabancin kasar da ta fi kowacce yawan al’umma a nahiyar Afirka, wadda ke fama da hauhawar farashin kayan masarufi, da karancin kudaden kasashen waje da tabarbarewar Naira, da rashin tsaro da kuma satar danyen mai.

Talla

Hukuncin da wasu alkalan kotun kolin guda bakwai suka yanke, wanda shine na karshe, ya biyo bayan wani salon da aka gani a zabukan da suka gabata na shugaban kasar da aka kalubalanta a gaban kotu. Babu wani yunƙurin soke sakamakon ta hanyar kotuna da ya yi nasara.

Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour ne suka zo na biyu da na uku a zaben watan Fabrairu, amma suka ki amincewa da sakamakon, suka kuma yi kira da a soke nasarar da Tinubu ya samu.

Tinubu ya naɗa sabbin kwamishinonin zaɓe a jihohi tara

Shugabannin ‘yan adawa biyu sun daukaka kara kan hukuncin da kotun ta yanke a ranar 6 ga watan Satumba wanda ta amince da nasarar Tinubu.

Talla

Alkalin kotun koli John Okoro ya ce “Babu cancantar su Atiku da Obi su daukaka karar, don haka yace sun yi watsi da ita.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...