Tinubu ya naɗa sabbin kwamishinonin zaɓe a jihohi tara

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da naɗin sabbin kwamishinonin hukumar zaɓe a wasu jihohin ƙasar tara.

Cikin wata sanarwa da fadar shugaban ta fitar mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale, ta ce Tinubu ya amince da naɗin sabbin kwamishinonin na tsawon wa’adin shekara biyar.

Talla

Sanarwar ta ce naɗin kwamishinonin sai ya samu amincewar majalisar dattawan ƙasar, bayan tantance su.

Sabbin kwamishinonin sun haɗar da:

Mista Isah Shaka Ehimeakne – Kwamishinan zaɓe na jihar Edo.

Mista Bamidele Agbede – Kwamishinan zaɓe na jihar Ekiti.

Yanzu-Yanzu: Kotun koli ta Sanya ranar da za ta yanke hukunci kan Atiku da Obi a kan Tinubu

Mista Jani Adamu Bello – Kwamishinan zaɓe na jihar Gombe.

Dakta Taiye Ilayasu – Kwamishinan zaɓe na jihar Kwara.

Dakta Bunmi Omoseyindemi – Kwamishinan zaɓe na jihar Lagos.

Alhaji Yahaya Bello – Kwamishinan zaɓe na jihar Nasarawa.

Farfesa Mohammed Yalwa – Kwamishinan zaɓe na jihar Niger.

Dakta Anugbum Onuoha – Kwamishinan zaɓe na jihar Rivers.

Mista Abubakar Fawa Dambo – Kwamishinan zaɓe na jihar Zamfara.

Talla

Shugaba Tinubu ya yi kira ga sabbin kwamishinonin da su nuna ƙwarewa a aikinsu tare da bin doka da oda wajen gudanar da ayyukansu.

Domin tabbatar da shirya sabbin sahihai kuma ingantattun zaɓuka da ba su da rikici a jihohinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnan Kano ya bayyana abun da gwamnatin za ta yi a filin Idi

  Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanar...

Ba zaben 2027 ne a gaba na ba – Tinubu

    Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu...

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma...

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya tura tawaga mai karfi wajen Abba Ganduje

Daga Rahama Umar Kwaru   Babban Daraktan Hukumar Samar da Wutar...