Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Majalisar Dokokin jihar kano ta amince zata gayyato matashin dan adaidaita sahu nan da ya tsinci Naira Miliyan 15 kuma ya mayarwa Mai shi.
Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Doguwa, Hon. Salisu Ibrahim Muhammad, ne yayi kira ga majalisar da ta gayyaci Salisu Auwalu wanda ya tsinci kudi kimanin naira miliyan 15 domin a karramashi a majalisar.
Shugaban majalisar, Jibril Ismail Falgore, yace zasu gayyaci matashin, kuma za suyi masa karo-karo cikin albashin su.
Yayin zaman majalisar, dan majalisa Muhammad ya ce matashin ya nuna tsantsar tawakkali da kuma hali na gari wajen mayar da kudaden idan aka yi la’akari da halin matsin da ake ciki, a don haka ya kamata majalisar ta karrama shi.
Da dumi-dumi: Kotu ta yanke hukunci kan zaɓen gwamnan jihar Zamfara
Wannan ce ta sa shugaban majalisar ya amince da bukatar, yayin da ya amince a gayyaci matashin sannan yayi alkawarin cewa majalisar zata tallafa masa.
Yanzu-Yanzu: Tinubu Yayi Sabbin Nade-nade a ofishin mataimakin Shugaban kasa
Tun da Salisu ya mayar da wadancan kudade al’umma da dama suka yi yaba masa tari da yi masa kyaututtuka kala-kala domin Kara masa kwarin gwiwar cigaba da zama mai amana.
Yanzu haka ma mun sami labarin mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya baiwa mahaifin matashin kyautar kayan abinci da da tufafi, domin karama musu kwarin gwiwar cigaba da yiwa ya’yansu tarbiyya.