Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Zamfara ta kori karar da jam’iyyar APC ta shigar, ta kuma tabbatar da nasarar Dauda Lawan, a matsayin halastaccen zababban Gwamnan jihar Zamfara.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana Dauda Lawan na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar, hakan tasa Bello Muhammad Matawalle na jam’iyyar APC ya shigar da kara Inda yake ƙalubalantar nasarar da Dauda Lawan ya samu a gaban kotu.
A zaman yanke hukunci da kotun ta yi yau a birnin Sokoto, ta ce Dauda shi ne ya samu ƙuri’u mafi yawa a zaɓen.
Tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle ne ya shigar da ƙara yana ƙalubalantar nasarar Dauda a kotun wadda ke zaman ta a birnin Sokoto.