Daga Hafsat Yusuf Sulaiman
Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane na tarayyar Nigeria Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ya yi alkawarin bin manufofin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu sau da kafa don samar da tsarin samar da gidaje masu inganci ga ‘yan Najeriya.
Ministan wanda ya bayyana hakan yayin wata liyafar karrama shi da rusasshiyar jam’iyyar ACN reshen Jihar Kano ta shirya, ya ce ya zama wajibi su yi aiki tukuru don ganin an kawo ci gaban da ake bukata a kasar nan ta fuskar samar da matsuguni da ci gaban birane a Nigeria.
Da dumi-dumi: An Sanya Ranar Yanke Hukuncin Zaɓen Gwamnan Zamfara
ATM Gwarzo wanda ya yaba da nadin Babban Ministan sa Arc. Ahmed Musa Dangiwa, ya bayyana shi a matsayin mutum mai kwarjini wanda zai iya kawo sauye-sauye masu kyau a tsarin samar da gidaje da ci gaban birane a kasar .
Ministan ya kara da cewa zai yi amfani da dimbin gogewar da babban Ministan yake da ita wajen kawo wa al’ummarsa ci gaba.
Ya mika godiyarsa ga wadanda suka shirya taron da kuma dukkan abokansa na siyasa da suka bayar da gudumawa wajen ganin an gudanar da bikin tare da yin alkawarin zama jakadan jihar kano na gari a kasa wajen sauke nauyin da aka dora masa.
Da yake jawabi a wajen taron, tsohon Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa, Sanata Bello Hayatu Gwarzo, ya bayyana nadin na ATM Gwarzo a matsayin abin da ya dace, inda ya ce shi hazikin shugaba ne kuma dan siyasa mai son cigaban al’umma.
Sauran wadanda suka yi jawabi a wajen taron sun hada da Alh. Auwalu Rimi Mai Shadda, sai Sakataren jam’iyyar APC na Jihar kano Hon. Ibrahim Zakari Sarina wanda ya wakilci shugaban jam’iyyar na jiha, da Kuma Alh. Ibrahim Dan’azumi Gwarzo tsohon kasafi da tsare-tsare na jihar kano da dai sauransu.