Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin Dr. Jamila Bio Ibrahim a matsayin ministar matasa, har zuwa lokacin da majalisar dattawan tarayyar Najeriya ta amince da ita.
Shugaban ya kara amincewa da nadin Mista Ayodele Olawande a matsayin karamin ministan matasa, har zuwa lokacin da majalisar dattawan tarayyar Najeriya ta amince da shi.
Kadaura24 ta rawaito Hakan dain na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban kasa Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.
Zamu samar da ingantacceen tsarin samar da gidaje ga yan Nigeria – ATM Gwarzo
Dokta Jamila Bio Ibrahim matashiyar likita ce kuma a baya-bayan nan ta taba rike mukamin shugabar kungiyar Matasa ta (PYWF). Ta kuma yi aiki a matsayin babbar mataimakiya ta musamman ga gwamnan jihar Kwara kan maradun ci gaba mai dorewa (SDGs).
Shi kuwa Mista Ayodele Olawande kwararre ne wajen sha’anin ciyar da al’umma kuma shugaban matasa a jam’iyyar APC mai mulki. Kwanan nan ya yi aiki a ofishin mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan kirkire-kirkire daga 2019 zuwa 2023.
Shugaba Tinubu ya bukaci wadanda aka nadan da su tabbatar da cewa suna nuna kwazo da kuma kawo cigaba ga matasan Najeriya.