Daga Khadija Abdullahi Aliyu
A kokarin cike gibi a harkar kiwon kaji da kasuwanci a Nigeria, Kamfanin Simintin Dangote ya fara koyawa Matasa sana’ar kiwon kaji .
Janar Manaja Mai kula da harkokin al’umma da aiyuka na musamman na kamfanin Mista Ademola Adeyemi, aikin wani bangare ne na shirin wayar da kan al’umma na shekarar 2023 ga matasa a cikin al’ummomin jihar Kogi.
Ya ce shiga tsakanin zai taimaka wa gwamnati wajen bunkasa harkokin kiwon kaji da kasuwancinsa
A cewarsa, kawo yanzu an dauki matasa 30 da aka zabo daga yankuna daban-daban.
Daliban Firamare Sama da Miliyan 5 Ake Da su a Kano, Miliyan 4 Daga Cikin su a Kasa Suke Zama
Mista Adeyemi ya ce al’ummomin da suka ci gajiyar shirin sun fito ne daga Oyo, Obajana, Iwaa da Apata.
“Ana sa ran horon zai taimaka wajen bunkasa samar da kaji, sarrafawa, da kuma samar da su,” in ji shi.
Al-ameen G-Fresh da Sadiya Haruna sun bayyana makomar Aurensu
A cewarsa, an mika wa wadanda suka ci gajiyar wannan bukin na Starter a wani taron da ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki.
Abubuwan da ke cikin fakitin, in ji shi, sun haɗa da: Wurin Kwanciyar Kaji, Cajin Baturi, Magungunan Ciyar da sauran kayan aikin aiki.
Ya ce Kwalejin Ilimi ta Kabba ita aka dorawa alhakin gudanar da horon a madadin kamfanin na Dangote.
Shugaban kwalejin, Dr. Jagboro Victoria Olusola (Mrs.) ya yabawa kamfanin simintin Dangote bisa wannan shiri na inganta rayuwar al’umma .