Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Zamfara ta sanya ranar Litinin 18 ga Satumba, 2023 a matsayin ranar da zata yanke hukuncin Shari’ar zaɓen gwamnan jihar.
Kadaura24 ta rawaito Idan za’a iya tunawa bayan kammala zaɓen gwamnan jihar Zamfara wanda hukumar zabe ta bayyana Dauda Lawan na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben, hakan tasa jam’iyyar APC ta shigar da Kara gaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar domin ƙalubalantar zaben.
Hukuncin kotun dai shi zai tabbatar da halastaccen wanda ya ci zaɓen, duk kuwa da cewa akwai damar daukaka kara ga duk wanda bai aminta da hukuncin kotun Sauraren Kararrakin Zaben Gwamnan ba .
Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya Baiwa Kwamishinonisa Sabon Umarni
Yanzu haka dai al’ummar jihar Zamfara suna dakon zuwan ranar litinin din domin hukuncin da kotun zata zartar.