Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA) ta yabawa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf kan matakin gaggawa da ya dauka na korar wasu mukarrabansa guda biyu sakamakon barazanar kisan alkalan kotunan sauraren kararrakin zaben da kuma kalaman batanci ga mataimakin shugaban kasa.
Kadaura24 ta rawaito, Idan dai za a iya tunawa, kwamishinan kasa da safayo, Adamu Aliyu Kibiya a ranar Alhamis a wani taron addu’a na musamman da magoya bayan jam’iyyar NNPP suka gudanar, inda ya yi barazana ga alkalan kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da cewa duk wanda a cikinsu ya karbi cin hanci don murde hukuncin sai dai ya zabi ko kuɗi ko rayuwarsa.
Har ila yau, mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin matasa da wasanni, Yusuf Imam, wanda aka fi sani da Ogan Boye, a wani faifan bidiyo a ranar Alhamis yayin taron addu’o’i na musamman da NNPP ta gudanar yayi kalaman batanci ga mataimakin shugaban kasa, Khasim Shettima da kuma tunzura al’umma.
Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya Baiwa Kwamishinonisa Sabon Umarni
Da yake zantawa da SOLACEBASE kan ci gaban, Shugaban kungiyar lauyoyin na Kano, Barr. Suleiman Gezawa ya yaba wa gwamnan jihar kan matakin korar mukararabanwa kan kalaman da sukai da kuma nisanta gwamnatinsa da kalaman da sukai .
Daga nan Gezawa ya yi kira ga jami’an tsaro da su kaddamar da bincike kan barazanar kisa da kwamishinan ya yi wata kila akwai wata makarkashiya a cikin wannan barazanar ta shi.