Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Shahararriyar jarumar Facebook da TikTok, Sayyada Sadiya Haruna ta bayyana cewa halin da ake ciki yanzu babu aure a tsakaninta da angonta, Al’ameen G-Fresh saboda ya sake ta tuntuni.
“Da bakin sa ya furta ya sake ni kuma ya dau kafarsa ya bar gidana, amma yaje yana cewa ni na kore shi “. ta ce.
Sadiya Haruna ta kuma ƙara da cewa G-Fresh ya buƙaci ta biya shi dukkan kuɗaɗensa da ya kashe wajen hidimar aurenta kuma ta ba shi.
Sadiya Haruna ta bayyana hakan ne yayin wata ganawa da tayi da Freedom Radio dake Kano a Nigeria.
Barazanar kisa: NBA ta yabawa Gwamnan Kano, ta bukaci jami’an tsaro su fara bincike
Sai dai kuma, a nasa ɓangaren, Al-Ameen G-Fresh ya bayyana cewa har yanzu akwai aurensa akan Sadiya Haruna kuma bai saki matarsa ba.
“Akwai aure a tsakaninmu wani ne dai da ke zaman P.A ɗinta ya ke hure mata kunne domin har abinci su ke ci tare ni kuma a matsayinna na mijinta ta zuba min nawa a wani kwanon na daban” a cewar G-Fresh
Da dumi-dumi: An Sanya Ranar Yanke Hukuncin Zaɓen Gwamnan Zamfara
“Kasan wasa to ko da wasa ban saki matata Sadiya Haruna ba, saboda auren soyayya mu ka yi, Kuma har yanzu Ina son ta”. A Cewar G-Fresh
A baya dai G-Fresh Al-ameen ya taba yin karar wani Abba Ado Wise ga hukumar Hisbah ta jihar kano saboda zarginsa da zuga tare da bibiyar sayyada Sadiya Haruna alhalin tana matar aure, wanda hakan tasa take yi masa abubun da basu dace ba.
Sai dai tun a baya Hukumar Hisba sai da a yiwa Abba Wise tsakani da Sadiya, amma daga bisani ta samu labarin bai mutunta yarjejeniyar ba, hakan kuma tasa hukumar ta kama shi tare da tsare shi a hukumar.