Ƙarin bayani akan dalilin gwamnatin Kano na korar kwamishinan da Oga Boye

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sallami kwamishinan filaye da safiyo na gwamnatin jihar, Adamu Aliyu Kibiya daga muƙaminsa, bayan zargin sa da furta kalaman tunzura al’umma.

Bugu da ƙari sallamar ta shafi mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin wasanni da matasa,Yusuf Imam, wanda aka fi sani da Ogan Boye wanda shi ma ake zargi da furta kalaman da ba su dace ba a madadin gwamnatin.

Talla

A ƙarshen makon nan ne bidiyon jami’an gwamnatin suka rinƙa yawo a shafukan sada zumunta, inda suke furta kalamai game da shari’ar da ake yi kan zaɓen gwamnan jihar da ya gabata.

A cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Baba Halilu Ɗantiye da kuma na shari’a Haruna Isa Dederi suka karanta a daren ranar Alhamis, sun ce jami’an gwamnatin sun yi magana ba tare da izinin gwamna ba, sun kuma yi kalamai na tunzura al’umma sannan kuma sun ci zarafin mataimakin shugaban ƙasar, Kashin Shettima.

A cikin kwanakin nan dai yanayin na siyasa ya ƙara zafafa gabanin hukuncin kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen gwamna na jihar.

Manyan jam’iyyu a jihar, NNPP da APC sun gudanar da addu’o’i da azumi domin neman nasara a shari’ar.

A baya dai ɗaya daga cikin alƙalan kotun ta yi zargin cewa akwai wasu da ke yunƙurin bai wa alƙalai da lauyoyin kotun cin hanci domin samun nasara a shari’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria

Matatar mai ta dangote ta rage farashin man fetur...

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...