Daga Hafsat Yusuf Sulaiman
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ce zai yiwa dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023 Alhaji Atiku Abubakar ritaya r siyasa kuma ya saya masa dabbobi don ya je yayi kiwonsu.
Shettima ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta tabbatar da nasarar da shugaba Bola Tinubu ya samu a kotun daukaka kara a ranar Laraba.

Bayan ya bayyana gamsuwarsa da hukuncin kotun da kuma yin kira ga abokan adawa da su hada kai da su, daya daga cikin ‘yan jarida ya tambaye shi ko har yanzu zai yi ritaya Atiku – daya daga cikin kalamansa a lokacin yakin neman zabe.
Da dumi-dumi: Bayan korar karar Atiku, Kotun ta tabbatar da nasarar Tinubu
Tsohon gwamnan jihar Borno ya ce, “Mun wuce matakin siyasa. Yanzu, muna cikin al’amuran mulki ne, Atiku Abubakar dattijo ne wanda nake matukar girmama shi.
“Duk wanda ya san yadda ake mu’amala da al’adu tsakanin Fulani da Kanuri a arewa, zai san cewa ina da ‘yancin yi masa wasa, kuma ya hakura.
“Ba za mu yi wa Atiku ritaya zuwa Dubai ko Morocco ba, zan yi masa ritaya ne zuwa Fombina. kuma zan sayo masa akuyoyi da kaji domin yaje ya cigaba da kiwonsu.

“A magana ta gaskiya Atiku dattijo ne da al’umma suke bukatarsa.
“Kwarewa ba abu bace da za ku iya saya a kasuwa ba. Mun amfana kwarai da tarin kwarewarsa da gogewarsa. Amma yanzu ya kamata ku sani yanzu lokacin siyasa ya wuce lokaci ne da zamu maida hankali wajen hidimtawa al’umma .”