Daga Zaiyad Isma’il
Wata kungiya mai zaman kanta mai suna yiwa Central and West African Virus Epidemiology, WAVE, a turanche, ta shirya taron wayar da kan manoma rogo kan sabuwar fasahar nomanan rogo a zamanance, domin kare amfanin da suka samu daga cututtuka dake shafarsu yayi shuka ba.
Taron wanda ya gudana a filin noman kungiyar na gwaji, wanda ke garin wuro biriji dake yankin Gawi na karamar hukumar Fufore a jihar Adamawa, taron kuma ya sami hallarta jami’an kungiyar WAVE, manoman rogo, shuwagabani gargajiya, dama sauran al’umma garin.

Yayin taron shugaban tawagar kungiyar, Abdulrahman Musa, ya bayyana cewa tawagar sun ziyarci garin wuro birijin ne domin wayarwa manoman kan sabuwar fasahar noman rogo, wacce zata kare amfanin noma daga cuttuka domin samun amfanin gona masu dumbin yawa.
” Yanzu lokaci ya wuce da za’a rika amfani da tsohon tsarin noman rogo, saboda amfani da dabarun zamani wajen noman rogo yana taimakawa wajen samun amfani Mai yawa da samun kudade masu zuwa”. Inji shi
Abdulrahman, ya kara da cewa muddin manoman sukayi amfani da sabuwar fasahar zamani da suka koyawa manoman, zasu samu dumbin ribar amfanin noman rogon da sukayi.
Abdullahi Idris da Hamman Adama Haruna na cikin manoma da suka hallarci taron wayar da kai, Wanda kungiyar wave tayi musu, inda suka yabawa kungiyar, bisaga gudumawar da suka basu na wayar musu da kai, a bangare noman rogo a zamanance, Wanda abaya basu samu makamancin Hakan ba .

Kana sunyi Kira ga mahukunta a jahar Adamawa dama sauran kungiyoyin masu zaman kansu da su kawo musu Tallafin domin bunkasa Harkan noman rogo.
Ana shi janabin wakilin mai garin gawi Malam Abubakar Aliyu, ya yabawa kungiyar ta wave da shirin wayarwa manomansu kai tare da Kira ga manoman garin dasuyi amfani da ilimin da suka koya wajen taron ta yadda yadace
Ita dai kungiyar wave wacce akafi saninta da Central and west Africa virus a turance kungiyar ce take aiki da gidauniyar tallafi ta Bill and Melinda gate wacce tayi hadaka da sauran kungiyoyin sa kai ta kasashen Birtaniya wacce ke fa manufar wayarwa manoman rogon kai kan sabuwar fasahar nomana rogo a zamanance domin amfanin manoma a kasashen yammaci afrika