Daga Zakariyya Adam Jigirya
Kotun sauraren kararrakin zabe ta Majalisar Dokoki a jihar Kano da ke ta ce AMuhammad Sanusi Said kiru na APC ya gaza wajen gabatar da hujjoji don tabbatar da cewa ba a yi sahihin zaben dan majalisar tarayya ba a kananan hukumomin Kiru/Bebeji, wanda ya baiwa Abdulmumini Jibrin Kofa na NNPP nasara.


Jagorar alkalan guda uku Mai Shari’a Ngozi Flora ta bayyana cewa takardun da bangarorin biyu suka gabatar a gaban kotun sun nuna cewa Abdulmumini Jibrin Kofa ya ajiye mukaminsa na Babban Sakataren Hukumar Gidajen Tarayya, kwanaki 30 gabanin gudanar da zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu 2023 a sabanin da’awar mai kara.
Mai shigar da kara ya kasa baiwa Kotun hujjojin cewa an tafka kura-kurai a zaben dan majalisar tarayya na Kiru da Bebeji ba, Inda yace ba’a bin dokar zabe ta 2022 ba a zaben.
Saboda haka mun kori wannan karar saboda rashin gamsassun hujjoji.

Kotun ta yi umarci wanda yayi kara da ya biya wanda akai Kara Kuɗin N100,000 .