Daga Hafsat Yusuf Sulaiman
Kungiyar ma’aikatan tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya a safiyar yau Talata ta dakatar da harkokin kasuwanci a tashoshin jiragen ruwa ta Apapa da Tin-Can Island na hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya NPA sakamakon shiga yajin aikin kwanaki biyu da kungiyar kwadago ta Najeriya ta kirawo a fadin kasar.
An ayyana yajin aikin gargadin ne domin nuna rashin amincewa da wahalhalun da ke yan Nigeria suke ciki sakamakon cire tallafin man fetur.

Rahotanni sun nuna cewa ma’aikatan sun rufe duk kofofin shiga tashoshin Apapa da Tin-Can Island .
NAFDAC ta yi Allah-wadai da masu amfani da wani sinadari wajen nunar da ‘ya’yan itatuwa
Hakan kuma ya sa an cunkoson ababen hawa a titin Mile 2 , yayin da ababen hawa suka ki daukar fasinjoji, lamarin da ya haifar da cikas a wasu ofisoshi da ke yankin Apapa.
Wani direban mota mai suna Yusuf Liadi ya bayyana cewa babu wata mota guda da ta tashi ko ta shiga tashar tun da safe saboda yajin aikin.

Jaridar kadaura24 ta ruwaito cewa kungiyar kwadago ta Najeriya NLC reshen jihar Kano a ranar Talata ta bi sahun takwarorinta na fadin Nigeria, waje shiga yajin aikin gargadi na kwanaki biyu don nuna rashin amincewa da cire tallafin man fetur da gwamnatin Najeriya Bola Tinubu ke jagoranta.
Rahotannin sun nuna cewa da safiyar ranar Talata ne kungiyar kwadago ta rufe wasu ofisoshin ma’aikatu da Hukumomin gwamnati dake a jihar.