Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) a ranar Litinin ta yi Allah wadai da amfani da sinadarin calcium carbide wajen saurin nunar da ‘ya’yan itatuwa.
Babbar daraktar hukumar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Christianah Adeyeye, ta yi Allah-wadai da lokacin kaddamar yayin bitar da NAFDAC ta shiryawa yan jaridu kan illolin da ke tattare da fataucin miyagun kwayoyi da kuma amfani da sinadarin Calcium Carbide wajen nika ‘ya’yan itatuwa wanda aka gudanar a garin Lafia na jihar Nasarawa.

“Akwai kiraye-kirayen da ‘yan Najeriya masu hankali suka yi kan bukatar daukar tsauraran matakai don dakile bala’in safarar miyagun kwayoyi da amfani da sinadarin calcium carbide wajen nika ‘ya’yan itatuwa.
Da dumi-dumi: Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa ta Bayyana Ranar da Zata Yanke Hukunci
“Bugu da kari, jaridu da dama a Nigeria da kungiyoyi masu zaman kansu sun nuna damuwa game da hadarin da ke kunno kai da hatsarin da za’a iya fadawa wadannan munanan ayyuka guda biyu da wasu marasa kishin kasa suke yi a Nigeria kawai saboda su sami kudi,” in ji ta.
Shugaban hukumar wanda ya samu wakilcin daraktan tantance sinadarai da bincike na hukumar, Dr Leonard Omokpariola, ya bayyana cewa, kaddamar da taron bitar wayar da kan ga yan jaridu, cika alkawarine da hukumar su ta yi na ci gaba da karfafa hadin gwiwar NAFDAC da kungiyar ‘yan jarida masu bada rahoton lafiya a Najeriya, wajen hada kai. ilimantarwa da wayar da kan ‘yan jaridun Najeriya da kuma wayar da kan ‘yan jaridun su taka rawar gani a kokarin da ake yi na kawar da matsalar fataucin miyagun kwayoyi da sanar da mutane Illar amfani da sinadarin Carbide wajen nunar da ‘ya’yan itatuwa ga lafiyar al’ummar Nigeria.

Adeyeye ya kara da cewa, barazanar safarar miyagun kwayoyi kalubale ne babba ga tsarin samar da kiwon lafiya a kasar wanda hakan zai tabbatar da kudurin hukumar NAFDAC na hana sayar da kwayoyi da sinadarin da suke cutar lafiyar al’umma .