Zamu fara kama masu yada jita-jitar wasu matsafa dake shanye jinin Mutane – Rundunar yan sandan Kano

Date:

 

Sakamakon jita-jitar da ta gauraye wasu sassan arewacin Najeriya game da wasu mutane da ake zargin masu shanye jini da ‘yan shafi mu-lera, ‘yan sanda sun fara yin dirar mikiya a kan wasu da ake zargin suna yaɗa irin wannan jita-jita, da kan janyo a far wa wasu mutane da ba su ji ba, ba su gani ba.

 

Ana ta yaɗa jita-jitar cewa wasu mata na yin sallama a gidajen mutane, inda suke roƙon ruwan sha, amma a cewar masu jita-jitar sai mutanen su zuƙe wa wanda ko wadda ta ba su ruwa jini.

Talla

A wata ruwayar kuma, an ce mutanen da ake zargi suna kwashe wa namiji mazakuta, yayin da mace take rasa mamanta.

BBC ta rawaito Irin wannan jita-jita dai, ta kai ga har cincirindon mutane suna far wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba a jihohi kamar Kano da Bauchi da Kaduna.

Da dumi-dumi: Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa ta Bayyana Ranar da Zata Yanke Hukunci

Sai dai a yanzu, hukumomi sun fara yin dirar mikiya a kan mutanen da ke yaɗa irin wannan jita-jita maras tushe.

Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta fitar, ta ce wannan lamari ya yi ƙamari ne tsakanin ranar Juma’a zuwa ranar Lahadi 3 ga watan Satumba.

Ta yi Allah-wadai da abin da ta kira “cin mutuncin matafiya da baƙin fuska” a unguwannin da ba a san su ba.

Jam’iyyar APC zata lashe zaben gwamnan Kogi da rinjaye mai yawa – Ganduje

Inda ta ce ta gudanar da bincike kan wasu daga cikin koken da aka shigar mata kuma ta gano duka zarge-zarge “ba su da tushe, balle makama, don haka, ƙarya ne”.

Sanarwar da kakakin rundunar a Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ta ce ” wasu ɓata gari ne ke neman ta da zaune-tsaye ta hanyar haifar da gaba da ƙiyayya da jefa tsoro da firgici a zukatan mutane domin hana zaman lafiya”.

‘Yan sandan Kano sun ce a ranar Lahadi sun kuɓutar da wasu ‘yan mata ƙanana guda uku da shekarunsu ba su wuce tsakanin 12 zuwa 15 ba, a unguwar Kwana Hudu cikin ƙaramar hukumar Nassarawa.

“Mun samu kira a ranar Lahadi cewa, an kama wasu ‘yan mata a wani gida da ke layin Ɗanfili, ana zarginsu da shan jini, nan da nan jami’ai suka garzaya suka ceto su aka tafi da su asibitin Gwagwarwa aka duba su, sannan aka sallame su.

“Bayan gudanar da bincike mun gano sun shiga wani gida ne neman cajin waya, lokacin da suke cajin sai ɗaya ta nemi ta shiga banɗaki, sai matar gidan ta kurma ihu don a kawo mata ɗauki, kuma da maƙwabta suka shiga suka yi wa yaran duka. Mijinta kuma ya kulle su a ɗaki.

“Bincikenmu ya gano cewa babu wanda (‘yan matan) suka taɓa, kawai zargi ne maras tushe, mun kama matar da mijin sannan mun kama wasu daga cikin waɗanda suka taimaka wajen yaɗa wannan jita-jita,” in ji sanarwar.

Talla

Haka kuma, irin wannan lamarin ya faru a unguwar Zango a ƙaramar hukumar Ungoggo, inda aka tsare wasu mata biyu bisa zargin ‘masu shan jini ne’.

“Bayan samun kiran waya, ‘yan sandan sun garzaya inda lamarin ya faru tare da ceto matan, sannan aka garzaya da su wani asibiti.

“Bincike ya tabbatar mana da babu abin da suka yi, kawai an fuskanci baƙin fuska ne a unguwar, amma an shawo kan lamarin,” in ji sanarwar.

Irin wannan ta sake faruwa a hotoro in ji ‘yan sandan na Kano, shi ma an kama mutum shida dalilin zargin wasu mata da aka yi wa duka saboda baƙin fuska ne a unguwar.

Rundunar ‘yan sandan ta yi alƙawarin kama duk masu yaɗa wannan jita-jita, kuma za ta ci gaba da kare dukkan waɗanda suke faɗawa tarkon ɓata-garin da ke neman haifar da tashin hankali a Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...

Da dumi-dumi: Wasu kungiyoyin APC a Kano sun fara kiraye-kirayen Abdullahi Abbas ya sauka daga shugaban jam’iyyar

Daga Hafsat Abdullahi Muhammad Kungiyoyin jam'iyyar APC da suka hadar...

Bayan Amincewar Kasar Saudia , an Sanya Ranar Binne Aminu Dantata a Madina

Babban sakataren marigayi Alhaji Aminu Dantata, Mustapha Abdullahi Junaid...

Rashin Alhaji Aminu Dantata Babban Rashi ne ga harkokin kasuwanci a Duniya – Salbas

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Babban kamfani a masana'antar mai a...