Mun Gano Masu Shirin yin Zanga-zangar Tashin Hankali a Nigeria – DSS

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta ce ta gano shirin da wasu mutane ke yi na gudanar da zanga-zangar tashin hankali a faɗin ƙasa domin nuna gazawar gwamnatin tarayya da kuma jami’an tsaro na magance batun matsin rayuwa da mutane ke ciki.

Talla

DSS ta ce tana sanya ido kan shugabannin kungiyoyin domin dakatar da su daga jefa ƙasar cikin zaman rashin doka.

Da dumi-dumi: Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa ta Bayyana Ranar da Zata Yanke Hukunci

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun DSS ɗin Peter Afunanya ya fitar, ta ce an samu bayanan sirri da ke nuna cewa mutane da ke shirin yin zanga-zangar sun kunshi wasu ƴan siyasa da ke haɗa kan shugabannin ɗailbai, kungiyoyin kabilu da matasa da kuma fusatattun kungiyoyi.

NNPP za ta binciki Kwankwaso da wasu kan zargin karkatar da kudin takarar N1b

Hukumar ta kuma shawarci shugabannin Jami’o’i da sauran makarantu da su ja hankalin ɗalibansu daga shiga cikin abubuwan da za su janyo rashin zaman lafiya.

Talla

Har ila yau, DSS ɗin ta buƙaci iyaye da su riƙa yi wa ‘ya’yansu nasiha na su guji shiga cikin abin da zai karya doka da oda.

Hukumar ta sha alwashin kama duk wanda ya yi ƙoƙarin tayar da zaune tsaye a faɗin ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...

Da dumi-dumi: Wasu kungiyoyin APC a Kano sun fara kiraye-kirayen Abdullahi Abbas ya sauka daga shugaban jam’iyyar

Daga Hafsat Abdullahi Muhammad Kungiyoyin jam'iyyar APC da suka hadar...

Bayan Amincewar Kasar Saudia , an Sanya Ranar Binne Aminu Dantata a Madina

Babban sakataren marigayi Alhaji Aminu Dantata, Mustapha Abdullahi Junaid...

Rashin Alhaji Aminu Dantata Babban Rashi ne ga harkokin kasuwanci a Duniya – Salbas

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Babban kamfani a masana'antar mai a...