Shugaba Tinubu ya yiwa yan Kano komai da ya baiwa Dr Mariya Bunkure Minista – Dr. Jibril Yusuf JY

Date:

 

Tsohon kwamishinan ma’aikatar harkokin Noma ta jihar kano Dr Jibril Yusuf JY ya ce nadin da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya yiwa Dr. Mariya Mahmoud Bunkure a matsayin minista abun a yaba masa ne.

 

” Mariya Mahmoud Bunkure macece da ta ke da hazaka da jajircewa wajen gudanar da aikin ta, don haka babu Shakka Mariya Mahmoud Bunkure ba za baiwa shugaban kasa da Mutanen jihar kano kunya ba”. Inji shi

Talla

” Dama mun zabi shugaban kasa Bola Tinubu ne don yayin aikin da zai bunkasa cigaban Nigeria, Kuma daga irin mutanen da ya dauko wanda zai nada su a matsayin ministocinsa mun san da gaske yake , domin ya debo yan kishin kasa Masu son cigaban al’umma musamman irin su Mariya Mahmoud Bunkure”. A cewar Dr. Jibril Yusuf JY

Ina da yaƙinin Ganduje zai kai APC ga Nasara a Nigeria – Dr. Jibril Yusuf JY

Dr. Jibril Yusuf JY ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24 daga kasar China.

Talla

Tsohon kwamishinan wanda shi ne jagoran jam’iyyar APC a kananan hukumomin Rano Kibiya da Bunkure yace yana da yaƙinin Mariya Mahmoud Bunkure zata iya sauke nauyin da shugaban kasa ya dora mata a duk ma’aikatar da aka tura ta domin yin aikin, saboda jajircewar ta.

” Ina amfani da Wannan dama a madadin ni kaina da iyali na da daukacin al’ummar kananan hukumomin Rano Kibiya da Bunkure da na jihar kano baki daya, Muna mika sakon godiya ga shugaban kasa da jagoranmu kuma Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje bisa yadda suka dubi cancantata wajen baiw yar yankin mu mukamin Minista”. Inji Jibril Yusuf JY

Ya kuma ce suna taya ta murna samun wannan mukami tare da yi mata addu’ar Allah ya bata ikon sauke nauyin da aka dora musu don ciyar da al’ummar Nigeria gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika sakon ta’aziyyar Rasuwar Aminu Dantata

Daga Sadiya Ahmad   Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika...

Kungiyar ’Yan Jaridun Kano Arewa ta Aike da Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Alhaji Aminu Dantata

  Kungiyar ’Yan Jarida ta Kano Arewa ta bayyana alhinin...

Ku na da rawar takawa wajen inganta Lafiyar al’ummar Kano – Waiya ga jami’an yada labarai

Daga Abubakar Sayeed Kwamishinan Ma'aikatar yada labarai da harkokin cikin...