Ina da yaƙinin Ganduje zai kai APC ga Nasara a Nigeria – Dr. Jibril Yusuf JY

Date:

Daga Aisha Muhammad Adam

 

Tsohon kwamishinan ma’aikatar harkokin Noma ta jihar kano Dr. Jibril Yusuf Rurum ya taya tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje murnar nadin da aka yi masa a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa.

 

“Muna da kwarin gwiwar sabon shugaban jam’iyyar na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje zai dora jam’iyyar APC kan turbar ci gaba da magance duk wasu rike-rikece, tare da shigo da yan jam’iyyun adawa cikin APC , saboda yana da kwarewa da gogewar Shugabanci”.

Talla

Dr. Jibril Yusuf wanda ake yiwa lakabi da JY ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da jaridar kadaura24 ta wayar tarho daga ƙasar China .

Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya yi sabbin nade-naden shugabannin ma’aikatu 15

Ya bayyana Ganduje a matsayin shugaba wanda ya samar da nasarori masu tarin yawa a lokacin da ya ke rike da kujerar gwamnan Kano .

“Ina da kwarin gwiwar cewa tsohon gwamnan ba shakka zai hada kan jam’iyyar tare da marawa gwamnatin shugaba Tinubu baya a shirye-shiryen sa na ciyar da Nigeria gaba da Kuma Kara inganta dimokaradiyyar Nigeria”. Inji Dr . Jibril Yusuf JY

Talla

Tsohon kwamishinan Noman wanda shi ne jagoran jam’iyyar APC a kananan hukumomin Rano Kibiya Bunkure yace jam’iyyar APC a hannun Ganduje zata kai matakin jam’iyyar da zata fi kowacce jam’iyya girma da buwaya a Africa baki daya, kuma hakan zai karawa dimokaradiyyar Nigeria kwari da girma an idanun duniya .

” A madadina da iyalai na da dukkanin al’ummar kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure Muna taya gwarzo hazikin jagora Dr. Abdullahi Umar Ganduje murnar wannan babban matsayi da ya samu, Muna addu’ar Allah ya taya shi riko ya bashi damar sauke nauyin da aka dora masa”. Inji Jibril Yusuf JY

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a ranar Alhamis din da ta gabata ne aka nada tsohon gwamnan jihar Kano, Ganduje a matsayin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC domin karbar ragamar shugabancin jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ana daf da yin jana’izar Aminu Dantata a Madina

Tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa Madina na...

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...

Da dumi-dumi: Wasu kungiyoyin APC a Kano sun fara kiraye-kirayen Abdullahi Abbas ya sauka daga shugaban jam’iyyar

Daga Hafsat Abdullahi Muhammad Kungiyoyin jam'iyyar APC da suka hadar...