Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, kuma tsohon gwamnan jihar kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ce surutan da mutanen jihar Kano suka rika yi a kafafen sada zumunta kan nadin Maryam Shetty ne suka sa Shugaban Kasa Bola Tinubu ya canza shawararsa a kan nada ta minista.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a ranar Larabar da ta gabata Shugaba Bola Tinubu ya aike da sunan Maryam Shetty da wasu mutum 18 domin nada su ministoci.
Kwankwaso ya Taya Ganduje Murnar zama Shugaban APC na Ƙasa
Sai dai aike wa da sunan Maryam Shettyn daga Kano ya janyo ce-ce-ku-ce musamman a kafafen sada zumunta a Jihar, inda kashegari Tinubu ya sanar da janye sunanta tare da maye gurbinta da Dokta Mariya Bunkure.
An dai yi ta zargin cewa Ganduje, ne ya taka muhimmiyar rawa wajen cire sunan Maryam din da kuma maye gurbinta da na Mariya Mahmoud Bunkure wacce tsohuwar Kwamishiniya ce a tsohuwar gwamnatinsa.

Yayin da yake ganawa da manema labarai a gidansa dake Abuja, Ganduje ya ce surutan da aka rika yi ne suka canza tunanin Tinubu akan Maryam Shetty.
Maryam Shetty ta Magantu kan Cire Sunanta daga Cikin Ministocin Tinubu
“Lokacin da aka bayyana sunanta, mutane sun yi ta ce-ce-ku-ce a soshiyal midiya, ka san kuma wadannan kafafen na da tasiri sosai. Sai Shugaban Kasa ya kira ni ya tambaye ni, ku kuka bayar da sunanta, na ce masa a’a” a cewar Ganduje

“Sai ya tambaye ni ko na santa, na ce ban santa ba, sai ya ce to yaya aka yi aka shigar da sunanta in ba daga wajenku yake ba?
“A nan ya janye sunanta, inda ya nemi shawarar wacce zai maye gurbinta, tun da dole ya ce mace yake so, sai muka ba shi sunan Dokta Mariya, tun da akalla ita mun yi aiki da ita, kuma mun san kwarewarta”. Inji Ganduje
Ganduje yace wajen zabarta, sun yi la’akari da yankin da ta fito na Kano ta Kudu, wanda ya sha korafin cewa a baya ana danne shi, “ka ga yanzu mun yi adalci ke nan.
Sai dai ya ce duk da haka, yana da kwarin gwiwar Shugaban Kasa ba zai bar Maryam din haka ba, zai ba ta wani muƙamin a nan gaba.