Wani da Rundunar yan sandan Kano take nema ruwa a jallo ya kai kansa

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

Wani mai suna Nasiru Abdullahi, wanda aka fi sani da Chile Maidoki, wanda yana cikin manyan mutane uku da rundunar ‘yan sandan jihar Kano take nema ruwa a jallo, ya mika kansa ga kwamishinan ‘yan sanda, Mohammed Usaini Gumel a ranar Asabar.

 

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa, Chile Maidoki, dan Layin Falwaya Kurna, na daga cikin manyan mutane uku da kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammad Gumel ya bayyana cewa rundunar su zata ba da ladan Naira 100,000 ga duk wanda ya kai kowanne daya daga cikin su.

Talla

Nasiru Abdullahi ya kai kan sa ne hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano dake Bompai a ranar Asabar.

Kwankwaso ya Taya Ganduje Murnar zama Shugaban APC na Ƙasa

Mika kan da Chile Maidoki ya yi shi ya kai adadin tubabbun masu laifi 100 da kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Mohammad Gumel ya karba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar kuma ya bayyanawa manema labarai a ranar Asabar.

Talla

“Chile Maidoki ya shaida wa ‘yan sanda cewa ya kan kwana a makabartar da ke cikin birnin Kano don kar jami’an tsaro su kama shi.

“Yanzu yana rokon ‘yan sanda da mutanen jihar da su yafe masa; ya tuba kuma a yanzu a shirye yake ya yi aiki da ‘yan sanda domin inganta zaman lafiya da ci gaba a jihar,” Kiyawa ya bayyana.

Don haka rundunar tace bai kamata mutane su kyamace shi ba.

“Duk da haka, sauran mutane biyun, har yanzu akwai ladan Naira 100,000:00 ga duk wanda ya kai bayanin yadda za’a kama su, kuma rundunar tana ci gaba da neman su.

Mutanen sune Abba Burakita na Dorayi Quarters da Hantar Daba na Kwanar Disu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...

Da dumi-dumi: Wasu kungiyoyin APC a Kano sun fara kiraye-kirayen Abdullahi Abbas ya sauka daga shugaban jam’iyyar

Daga Hafsat Abdullahi Muhammad Kungiyoyin jam'iyyar APC da suka hadar...

Bayan Amincewar Kasar Saudia , an Sanya Ranar Binne Aminu Dantata a Madina

Babban sakataren marigayi Alhaji Aminu Dantata, Mustapha Abdullahi Junaid...

Rashin Alhaji Aminu Dantata Babban Rashi ne ga harkokin kasuwanci a Duniya – Salbas

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Babban kamfani a masana'antar mai a...