Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Tsohon kwamishinan ma’aikatar raya karkara ta jihar kano Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso ya taya tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje murnar nadin da aka yi masa a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.
“Muna da kwarin gwiwar sabon shugaban jam’iyyar na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje zai dora jam’iyyar APC kan turbar ci gaba da magance duk wasu rike-rikece na nan da can a fadin Nigeria, saboda yana da kwarewa da gogewar Shugabanci”.

Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da jaridar kadaura24 a Kano.
Kungiyar Sanatocin Arewacin Nigeria ta yi gargadi kan daukar matakin soji a Jamhuriyar Nijar
Ya bayyana Ganduje a matsayin shugaba wanda nasarorin da aka samu a matsayinsa na gwamnan Kano har yanzu ba za su misaltuwa.
Maryam Shetty ta Magantu kan Cire Sunanta daga Cikin Ministocin Tinubu
“Ina da kwarin gwiwar cewa tsohon gwamnan ba shakka zai hada kan jam’iyyar tare da marawa gwamnatin shugaba Tinubu baya a shirye-shiryen sa na ciyar da Nigeria gaba da Kuma Kara inganta dimokaradiyyar kasar”. Inji Musa Iliyasu Kwankwaso

Musa Iliyasu Kwankwaso wanda shi ne ya yiwa jam’iyyar APC takarar dan majalisar tarayya a kananan hukumomin kura madobi da garum Malam ya kuma taya sabbin Ministocin da Tinubu ya zama daga kano murna, tare da addu’ar Allah ya basu ikon sauke nauyin da shugaban kasa Bola Tinubu ya dora musu.
” Tsohon mataimakin gwamna Engr. Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo da Dr. Mariya Mahmoud Bunkure, duk hazikai ne Masu son cigaba, saboda duk mun yi aiki da su don haka nasan suna da gudunmawar da zasu bayar don inganta rayuwar al’ummar Nigeria fiye da yadda sukai a kano”. Inii Kwankwaso
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a ranar Alhamis din da ta gabata ne aka nada tsohon gwamnan jihar Kano, Ganduje a matsayin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC domin karbar ragamar shugabancin jam’iyyar.