Daga Hafsat Lawan Sheka
Kungiyar shugabannin jam’iyyar NNPP na jihohi ta bukaci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Sanata Rabi’u Kwankwaso da ya yi murabus cikin gaggawa ko kuma a dakatar da shi har a bada daga jam’iyyar, NNPP bisa zarginsa da zagon kasa a zaben da ya gabata.
Jaridar Kadaura24 ta ruwaito cewa shugabannin jam’iyyar sun nemi a yi musu cikakken bayani kan alakar dake tsakanin Kwankwaso da jam’iyyar APC a lokacin da kuma bayan babban zaben kasar na 2023.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar Kwamared Sunday Oginni ya fitar ya zargi Kwankwaso da laifin kitsa rikicin NNPP a fadin kasar nan a wani yunkuri na kwace jam’iyyar daga hannun ainihin mai ita da kuma wadanda suka kafa jam’iyyar.
Juyin Mulki: Abdulsalami Abubakar, da Sarkin Musulmin Nigeria sun dira a Jamhuriyar Nijar
Sanarwar ta zargi cewa Kwankwaso yana amfani da dandamalin NNPP ne kawai wajen samar was kansa mafita a fagen siyasar Najeriya.
Ya yi nuni da cewa tarurrukan da Kwankwaso ke yawan yi da shugaban kasa Bola Tinubu wani abu ne dake tabbatar da yana yiwa jam’iyyar zagon kasa wanda kuma shugabannin jam’iyyar ba za su lamunci hakan ba.
Yanzu-Yanzu: An tabbatar da Ganduje a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC
Sanarwar ta ce shugabannin jam’iyyar NNPP sun gano cewa Kwankwaso tare da hadin gwiwar kungiyarsa sun yi wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar kwaskwarima domin su taimaka a yunkurinsu na kwace jam’iyyar.
“Hakazalika, rashin bin ka’idar tsarin mulki na baya-bayan nan da aka ce sun yi na rusa shugabannin jihohi bakwai na Ekiti da Enugu da Neja da Kaduna Katsina da Ribas da Zamfara tun daga matakin jiha da kananan hukumomi har zuwa mazabu a lokaci guda abu ne da ba za a amince da shi ba.
“Kungiyar shugabannin jam’iyyar NNPP na jihohi muna amfani da wannan dama domin yin kira ga wanda ya assasa wannan babbar jam’iyya Dr. Boniface Aniebonam ya tashi tsaye wajen ganin ya janye yarjejeniyar fahimtar junan da suka yi da Kwankwaso ya dawo mana da jam’iyyar mu.
“Muna amfani da wannan damar don yin kira ga ‘yan Najeriya da su kasance masu hakuri da addu’a don ganin jam’iyyar ta Sami nasara a nan gaba don samar da sabuwar Najeriyar.”