Daga Sani Idris Maiwaya
Kungiyar Sanatocin Arewacin Nigeria ta yi gargadi kan amfani da karfin soji wajen tunkarar juyin mulkin da sojoji suka yi a jamhuriyar Nijar, tare da yin kira da a zabi hanyoyin diflomasiyya don warware lamarin.
Sanatan Kano ta kudu dan jam’iyyar NNPP. Suleiman Kawu, wanda shi ne mai magana da yawun kungiyar, shi ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Juma’a.
“Kungiyar a karkashin jagorancin Sen. Abdul Ningi (PDP-Bauchi), tace ta yi Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar, inda sojoji suka hambarar da gwamnatin dimokuradiyya ta shugaba Mohamed Bazoum .

Kawu Sumaila yace su Sanatocin Arewa sun fahimci irin kokarin da shugabannin ECOWAS ke yi a karkashin Jagorancin Shugaban mu, Bola Tinubu, wajen magance matsalar Jamhuriyar Nijar.
“Duk da haka, abin da ya fi muhimmanci shi ne, ya kamata mu mai da hankali wajen yin amfani da hanyoyin siyasa da diflomasiyya don mayar da mulkin dimokradiyy Jamhuriyar Nijar,” in ji shi.
Maryam Shetty ta Magantu kan Cire Sunanta daga Cikin Ministocin Tinubu
Kawu ya kara da cewa: “Ba kuma ma goyon bayan yin amfani da karfin soji har sai an gwada amfani da hanyoyin diflomasiyya abun ya ci tura, sakamakon amfani da karfin sojin zai haifar da asarar rayukan ‘yan kasar da ba su ji ba ba su gani ba, wadanda ke gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
“Bayan haka, kusan jihohi bakwai na Arewa ne ke iyaka da Jamhuriyar Nijar wato Sokoto, Kebbi, Katsina, Zamfara, Jigawa, Yobe da Borno, kuma idan akai amfani da karfin sojin abun zai shafe su kuma yayi musu mummunar illa.
Yanzu-Yanzu: Tinubu ya sauya sunan Maryam Shetty daga Ministocinsa
“Muna sane da halin da ake ciki a Mali, Burkina Faso da Libya, wanda zai iya shafar jihohin arewacin kasar bakwai, idan aka yi amfani da karfin soji.”
“A matsayinmu na ‘yan dimokradiyya da wakilan jama’a, muna kira ga abokan aikin mu da su lura yadda ya kamata, tare da yin la’akari da sashe na 5 karamin sashe (4) (a) da (b),” inji shi.