Yanzu-Yanzu: An tabbatar da Ganduje a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC

Date:

Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC a Najeriya ya tabbatar da zaɓen Dakta Abdullahi Umar Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano, a matsayin sabon shugaban riƙo na jam’iyyar.

 

Shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu na cikin manyan ƙusoshin jam’iyyar da suka halarci taron kwamitin zartarwar APC na ranar Alhamis.

Talla

An zaɓi Ganduje ne a lokacin taron kwamitin gudanarwar jam’iyyar na 12 da aka gudanar a otal ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja babban birnin ƙasar.

Cikakkun sunayen ministocin Tinubu guda 47 da Jihohin su

Tun da musalin karfe 9:30 ne mambobin kwamitin suka fara halartar ɗakin taron da ke otal din Transcorp Hilton, da ke Abuja babban birnin ƙasar.

Ranar 17 ga watan Yuli Shugaban jam’iyar na ƙasar sanata Abdullahi Adamu da babban sakaraten jam’iyyar Sanata Iyiola Omisore suka sanar da ajiye muƙamansu na shugabancin jam’iyar.

Inda jam’iyyar ta sanar da naɗin Sanata Abubakar Kyari, wanda shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar shiyyar arewacin ƙasar, a matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar.

To sai dai a ranar 27 ga watan Yuli ne shugaban ƙasar Bola Tinubu ya sanya sunan Sanata Abubakar Kyari cikin jerin sunayen da ya aika Majalisar Dattawan ƙasar don tantance su a matsayin ministocin gwamnatinsa.

Tun bayan saukar Abdullahi Adamu ne ake ta raɗe-raɗin cewar Abdullahi Ganduje ne zai maye gurbinsa a matsayin sabon shugaban riko na jam’iyyar.

Gabanin hakan dai ana ta ce-ce-ku-ce kan ko sunan tsohon gwamnan na Kano, kuma ɗaya daga cikin manyan na-hannun daman shugaban ƙasar, yana cikin waɗanda Tinubun zai bai wa muƙamin minista, musamman saboda rawar da ya taka tun farko wajen samun nasarar shugaban ƙasar a zaɓen 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika sakon ta’aziyyar Rasuwar Aminu Dantata

Daga Sadiya Ahmad   Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika...

Kungiyar ’Yan Jaridun Kano Arewa ta Aike da Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Alhaji Aminu Dantata

  Kungiyar ’Yan Jarida ta Kano Arewa ta bayyana alhinin...

Ku na da rawar takawa wajen inganta Lafiyar al’ummar Kano – Waiya ga jami’an yada labarai

Daga Abubakar Sayeed Kwamishinan Ma'aikatar yada labarai da harkokin cikin...