Daga Rahama Umar Kwaru
Shugaban Nigeria Bola Tinubu ya tabbatar wa shugabannin kungiyar kwadago cewa matatar mai ta Fatakwal za ta fara aiki nan da watan Disamba na Shekarar 2023.
Kungiyar kwadagon ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a daren Laraba, a Abuja bayan wata ganawa da suka yi da shugaba Bola Tinubu.

Shugabannin kwadagon sun kuma bayyana cewa, shugaban ya yi alkawura da dama inda suka amince da komawa kan teburin tattaunawa.
Cikakkun sunayen ministocin Tinubu guda 47 da Jihohin su
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya, Joe Ajaero da Trade Union Congress, Festus Osifo suka fitar.
Sanarwar ta kuma yabawa ‘yan Najeriya bisa goyon bayan zanga-zangar da suka yi a fadin kasar.