Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Shugaban kasar Nigeria Bola Tinubu ya zuwa yanzu ya tura sunayen wadanda yake son nadawa mukaman ministoci su 47 ga majalisar dattawan Nigeria domin tantancewa.
Tinubu ya tura sunayen ne kashi biyu, a rukunin farko ya turawa Majalisar sunayen mutane 28 wadanda tuni majalisar ta kammala tantance su kuma ta amince a nada su.

Kadaura24 ta rawaito sai kuma rukunin na biyu su 19 da aka turawa majalisar a jiya laraba 02 ga watan Ogusta, 2023, kuma tuni majalisar tace su fara zuwa gabanta domin tantancesu daga gobe juma’a.
Ga cikakken kunshin sunayen ministocin 47 da jihar da kowanne ya fito:
Shugabancin APC: Kwamitin zartarwar Jam’iyyar Zai Amince Da Nadin Ganduje A Yau
Akwa Ibom: Ekperikpe Ekpo
Bayelsa: Heineken Lolokpobri
Cross River: Betta Edu
Cross River: John Enoh
Delta: Stella Okotete
Edo: Abubakar Momoh
Rivers: Nyesom Wike
Adamawa: Tahir Mamman
Bauchi: Yusuf M Tuggar
Bauchi: Ali Pate
Borno: Abubakar Kyari
Gombe: Alkali Ahmed Saidu
Taraba: Uba Maigari Ahmadu
Yobe: Ibrahim Geidam
Taraba: Sani A Danladi
Jigawa: Mohamed Badaru
Kaduna: Nasir El-Rufai
Kano: Maryam Shetty
Kano: Abdullahi T Gwarzo
Katsina: Ahmad Dangiwa
Katsina: Hanatu Musawa
Kebbi: Yusuf Tanko Sununu
Kebbi: Atiku Bagudu
Sokoto: Bello M Goronyo
Zamfara: Bello Matawwalle
Abia: Nkiru Onyejiocha
Anambra: Uju Ohaneye
Ebonyi: David Umahi
Enugu: Uche Nnaji
Imo: Doris Uzoka
Ekiti: Dele Alake
Lagos: Tunji Alausa
Lagos: Lola Ade John
Ogun: Ishak Salako
Ogun: Bosun Tijjani
Ogun: Olawale Edun
Ondo: Olubunmi Tunji-Ojo
Osun: Adegboyega Oyetola
Oyo: Adebayo Adelabu
Benue: Joseph Utsev
FCT: Zaphaniah Bitrus Jisalo
Kogi: Shuaibu A Audu
Kwara: Lateef Fagbemi
Nasarawa: Imaan S-Ibrahim
Niger: Mohammed Idris
Niger: Aliyu Sabi Abdullahi
Plateau: Simon Lalong
Al’ummar Nigeria dai sun kaga a rantsar da ministocin da Kuma ma’aikatun da za’a tura su.