Hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano ta Kama Mutane 8, kan zargin batan biliyan 4 a KASCO

Date:

Daga Zainab Kabir Kundila

 

Hukumar karɓar korafe-korafenda hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta ce ta fara binciken batan wasu kudaden gwamnati sama da Naira biliyan 4 da suka bata a kamfanin samar da kayan noma na jihar Kano, (KASCO).

 

Rimin Gado ya ce an karkatar da kudaden ne daga kamfanin KASCO zuwa wata kungiya mai rijista da Hukumar Kula da Kamfanoni ta kasa, mai suna Association of Compassionate Friends.

Talla

Majiyar Kadaura24 ta Solacebase ta rawaito, shugaban hukumar Barr. Muhuyi Magaji Rimin gado ne ya tabbatar da haka a lokacin da ya jagoranci wani ayarin masu bincike zuwa inda aka ajiye motoci da manyan taraktoci da ake zargin an sayo su ne da kudaden da aka bankado a karamar hukumar Kumbotso ta jihar.

 

“An samar da kungiyar ne don inganta tare da kula da rayuwar ‘ya’yan marasa galihu a cikin al’umma, amma abin takaici sai aka mayar da ita wata hanya ta satar dukiyar al’umma,” a cewar Muhuyi.

Shari’ar zaɓen gwamnan kano: Abba Gida-gida ya daukaka kara akan Shaidar APC na 32

“Gwamnatin jihar Kano ce ta bada wadannan kudade a matsayin tallafi ga hukumar KASCO, amma an zaftare su ne ta hanyar amfani da kamfani mai rijistar yin harkokin kasuwanci .

“Mun kama mutane takwas da ake zargi domin su bamu sahihan bayanai don saukaka aiyukan hukumarmu. Daya daga cikin su ya ce an ba shi wasu kudi ne da sunan KASCO, amma ya ajiye kudin a gefe yana jiran lokaci kamar wannan, kuma da mayar da kudin.

“Ya zuwa yanzu, mun kwato Naira miliyan 15 kuma mun yi nasarar hana fitar da kusan Naira miliyan 8,” in Rimin Gado

Muhuyi Magaji ya ce hukumar na da shakkun yadda akai hada-hadar kudade tsakanin kamfanin da wasu bankuna, yana mai jaddada cewa za a iya gayyatar wasu manajojin bankin domin warware wasu batutuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...