Da dumi-dumi: Jami’an tsaron Najeriya sun ba hammata iska kan Emefiele

Date:

 

Jami’an hukumar tsaron fari kaya ta Najeriya, DSS da jami’an ganduroba sun yi arangama a babbar kotun tarayya da ke Legas kan tsare gwamnan babban bankin kasar da aka dakatar, Godwin Emefiele.

Kotun ta yanke hukunci da cewa dakatar Emefiele ya ci gaba da zama a gidan yari na Ikoyi da ke Legas har sai ya cika belin da aka ba shi a kan kudi Naira miliyan 20.

Talla

BBC Hausa ta Jami’an DSS sun matsa kaimi wajen sake kama Mista Emefiele bayan shari’ar kotun da ta kai ga yin kace-nace tsakanin jami’an tsaron biyu.

An tuhumi Emefiele da laifin mallakar bindiga da harsasai daga hukumar DSS ba bisa ka’ida ba. Zargin da ya musanta.

Wani lauya a Kano ya nemi yan sanda su baiwa A.A Rufa’i kariya, tare da bincikar masu tunzura shi

Mai shari’a Nicholas Oweibo ne ya bayar da belin Emefiele, mai shekaru 61, wanda ya yi watsi da ikirarin da gwamnati ta yi na cewa zai iya tserewa zuwa wani ƙasa idan ya sami sarari.

An dage sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano za ta fara jiyo ra’ayoyin al’umma kafin gudanar da duk wani aiki a jihar – Bilkisu Indabo

Daga Samira Hassan   Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin nan...

Kwankwaso ya gana da Tinubu a fadar shugaban kasa

Daga Nasiba Rabi'u Yusuf   Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso,...

Neman Ilimin addini dana boko da sana’a ba kishiyoyin juna ba ne – Dr. Aminu Sagagi ga matasan Zango

Daga Rahama Umar Kwaru   Wani Malamin addinin musulunci a kano...