Shari’ar zaɓen gwamnan Kano: Gawuna bai taya Abba murnar cin zabe ba – Rabi’u Bichi ya fadawa Kotu

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Wakilin jam’iyyar APC a zaben gwamna na 2023 a Kano, Rabiu Suleiman Bichi, ya ce dan takarar gwamnan jam’iyyar, Nasiru Yusuf Gawuna, bai taya abokin hamayyarsa na NNPP, Abba Kabir Yusuf murnar lashe zabe ba.

 

Rabi’u Bichi, wanda shi ne shaida na 31 da aka gabatar a gaban kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan Kano, ya bayyana hakan ne a yayin da ake masa tambayoyi a gaban kotun.

Talla

A zaman da aka koma ranar Asabar, lauyan mai shigar da kara, Offiong Offiong, Babban Lauyan Najeriya (SAN), wanda ya jagoranci shaidu, ya gabatar da shaida na 31 da shaida na 32.

 

Solacebase ta rawaito shaida na 31, Rabiu Suleiman Bichi, dan siyasa kuma wakilin jam’iyyar APC , a cikin sanarwar da ya yi a ranar 9 ga Afrilu, ya ce ya mika jerin sunayen wakilan jam’iyyar ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

Mun shirya maye gurbin labaran karya Dana Gaskiya a Social media – Kungiyar ASKOJ

Ya ce yana wurin taron manema labarai da jam’iyyar APC ta yi bayan zaben, amma bai ji lokacin da Gawuna ya taya Abba Kabir Yusuf murna ba.

Yanzu-Yanzu: Yadda Tinubu zai samar da hukumar kula da farashin abinci a Nigeria

Idan dai za a iya tunawa, Gawuna a cikin wani sakon murya da babban Sakataren yada labaran da Hassan Musa Fagge ya aikewa a kafafen yada labarai ciki har da Kadaura24, Gawuna ya amince da sakamakon zaɓen tare da taya Abba murna tare da addu’ar Allah ya yi masa jagora.

A cewar sanarwar, “Ina taya shi murna, kuma ina addu’ar Allah ya shiriyar gwamnatinsa.

“Da farko dai mun roki Allah ya zaba mana abin da ya fi dacewa da mu, domin shi ne madaukaki mai bada mulki ga wanda ya so”.

Tun da farko gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mika takardar shaidar sunayen mambobin jam’iyyar NNPP a gaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano a matsayin baje koli.

Idan zaku iya tunawa a ranar 9 ga watan Afrilu ne jam’iyyar APC ta shigar da kara inda take kalubalantar hukumar zabe ta INEC kan bayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan kano da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.

Tawagar alkalan mai mutum uku karkashin jagorancin mai shari’a Oluyemi Akintan Osadebay, ta dage ci gaba da sauraren Shari’ar zuwa ranar 20 ga watan Yuli.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...