ASUU tace shirin bayar da bashin karatu ga ɗalibai a Nigeria ba mai ɗorewa ba ne

Date:

Kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya sauya dokar ba da bashin karatu ga dalibai da ya amince da ita, zuwa tallafin karatu domin bai wa ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi damar samun ilmi mai zurfi.

Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce, “tunanin bayar da bashin karatu ga dalibai ya zo ne a 1972 kuma yana cikin harkokin bankuna da aka kafa”.

A wata hira da da gidan Talbijin na Channels ranar Lahadi, shugaban ASUU ya ce bashin karatun ba abu ne mai yiwu ba. A cewarsa, bayar da bashi don yin karatu “ba zai dore ba”

Yanzu-Yanzu: Saudiyya ta bayyana ranar da za’a yi Arfa da Babbar Sallah

Ya yi iƙirarin cewa mutanen da suka karɓi bashin, ba su taɓa biya ba, kuna iya zuwa ku bincika. A shekarar 1994 ko 1993, sojoji sun kafa dokar soja mai lamba inbda suka kafa hukumar bayar da bashi ga ɗalibai. Sai Majalisar dokoki ta daidaita ta a shekara ta 2004 kuma a cikin shekara ɗaya, ta wargaje. Kuɗaɗen suka bace. Muna so mu ga yadda wannan zai bambanta”.

A cewarsa, akwai dalibai sama da miliyan daya a jami’o’in gwamnatin Najeriya kuma rancen ba zai iya biyan kudin karatun dalibai ba.

Kungiyar ƙwadago ta bayyana dalilan da suka sa ta janye tafiya yajin

A ranar Litinin ne Shugaba Tinubu ya sa hannu a kan dokar ba da bashi ga dalibai domin cika alƙawarin da ya dauka a lokacin yaƙin neman zabensa.

Tallah

Shugaban majalisar wakilai ta 9, Femi Gbajabiamila, wanda yanzu shi ne shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa ne ya dauki nauyin gabatar da ƙudurin dokar a majalisa.

Dokar ta tanadi ba da bashi maras ruwa ga daliba masu ƙaramin ƙarfi a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...