KEDCO sun bayyana dalilin da yasa ake fuskanta rashin wuta a Kano, Jigawa da Kaduna

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Kamfanin KEDCO ya bayyana cewa matsalar da wasu turakun watu dake tunkudo wutar lantarki daga babban tashar samar da wutar dake shiroro ne yasa ake fuskantar matsalar rashin wutar lantarki a jihar kano Jigawa da kaduna.

 

“Kamfanin samar da wutar lantarki na kasa wato TCN ya sanar da mu cewa yana cigaba da aikin gyara turakunsu da suka sami matsala a shiroro, kuma muna sa ran za’a kammala aikin a wannan rana ta Lahadi”.

Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya yi sabbin nade-naden mukamai

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban sashin yada labarai da hulda da jama’a na kamfanin KEDCO Sani Bala Sani ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikewa manema labarai a Kano.

Tallah

Sanarwar ta baiwa al’ummar jihohin Kano Jigawa da Kaduna tabbacin zasu saki wutar lantarkin da zarar an kammala gyaran da ake yi a wannan rana.

KEDCO sun hakurkurtar da al’umma bisa matsalar da aka samu ta daukewa wutar lantarki a Wadancan jihohi.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a yan kwanakin al’ummar jihohin Kano Jigawa da kaduna suna fuskantar matsalar rashin wutar lantarkin wanda hakan ya kawo tsaiko a al’amura da dama

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba zaben 2027 ne a gaba na ba – Tinubu

    Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu...

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma...

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya tura tawaga mai karfi wajen Abba Ganduje

Daga Rahama Umar Kwaru   Babban Daraktan Hukumar Samar da Wutar...

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...