Daga Abdulmajid Habib Isa Tukuntawa
Kungiyar tsofaffin dalibai jami’an Maryam Abacha da suka yi karatun aikin jinya wato Nursing Association of MAAUN ta kai wata ziyara ta wayar da kan daliban makarantar mata ta Kano Capital Girls Secondary School .
Da yake yiwa wakilin Kadaura24 karin bayani kakakin kungiyar Sadiq Abubakar Ado yace sun shirya taron wayar da kan matan ne domin sanar da su hanyoyin da zasu kare kansu daga cututtuka musamman masu yaduwa.
” Da yake mata suna jinin al’ada to akwai bukatar matan su San yadda zasu kula da kansu saboda lokaci ne da zasu iya daukar cututtuka saboda yanayin halittarsu”. Inji Sadiq Ado
Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya bayyana ranar da zai mikawa majalisa sunayen kwamishinonini
Yace mata da yawa su kan dauki cututtuka a bandaki wato UTI Impection wanda hakan yakan haifar musu da matsalolin, hakan ce tasa suka je makarantar domin wayar da kan su don su gojewa duk abubuwan da ka iya haifar musu da matsala.
” Wannan aiki da mukai na tallafawa al’umma Mai makarantar mu ta MAAUN Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo saboda mutum ne Mai tallafawa al’umma shi yasa muka ga dacewar mu yi koyi da shi daidai karfinmu tunda ba za mu iya yin yadda yake yi ba”. A cewar kakakin kungiyar
Gwamnatin Kano za ta rushe Masarautun Gaya, Rano, Bichi da Karaye da Kuma dawo da Sarki Sunusi
Sadiq Abubakar Ado ya kara da cewa a lokacin watan Ramadana sun kai tallafi gidan marayu, shi yasa a wannan karon suka kai wancan tallafi makarantar Kano Capital, Inda suka raba audugar mata ga mata 50 .
Wakiliyar shugabar makarantar ta kano Capital Hajiya Maimuna Nuhu tace sunyi farin ciki da zuwan wannan kungiya makarantar da suka yadda suka wayar da kan daliban da Kuma kayan da suka raba musu

“Ya kamata sauran kungiyoyin tsofaffin dalibai su yi koyi da kungiyar tsofaffin daliban jami’ar MAAUN don tallafawa al’umma da ilimin da suka samu da Kuma dan abun da suke da shi”. A cewar Maimuna Nuhu
Hajiya Maimuna Nuhu ta yi fatan kungiyar baza ta gajiya ba wajen yin irin wannan aikin alkhairi, sannan ta hori daliban da su yi amfani da ilimin da suka samu don kare kawunansu daga kamuwa da cututtuka.
Suma wasu daga cikin daliban da suka samin tallafin sun nuna farin cikin tare da godewa wannan kungiya.