Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da dakatar da AbdulRasheed Bawa, a matsayin shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, domin ba da damar gudanar da bincike a kan yadda ya tafiyar da shugabancin sa.
Sanarwar da Daraktan yada labarai na fadar gwamnatin tarayya Willie Bassey, yace hakan ya biyo bayan zarge-zargen cin zarafi da aka yi masa.
An umurci Bawa da ya gaggauta mika ayyukan ofishinsa ga Daraktan Ayyuka a Hukumar, wanda zai kula da harkokin ofishin Shugaban Hukumar har sai an kammala bincike.