Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Hukumar tsaron farin kaya ta DSS yanzu haka ta na tsare da dakataccen Shugaban Hukumar yaki da hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC Abdulrashid Bawa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Bawa ya je helkwatar hukumar ta DSS da misalin karfe 09:02 na daren jiya laraba.
Gwamnatin Kano za ta rushe Masarautun Gaya, Rano, Bichi da Karaye da Kuma dawo da Sarki Sunusi
Wata majiya ta ce a halin yanzu jami’an ‘yan sanda na sirri suna tsare da shi bayan ya amsa gayyatar da sukai masa.
Hotuna: yadda Aka rushe shatale-talen dake Kofar gidan gwamnatin kano
Kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya, ya tabbatar wa Daily trust cewa Abdulrashid Bawa ya amsa gayyatar, kuma gayyatar ta Bawa tana da nasa da zarge-zargen da ake yi masa .