Daga Rukayya Abdullahi Aliyu
Jam’iyyar PDP ta koka kan wani shiri na kama wasu zababbun ‘yan majalisarta da ke neman ‘yancin cin gashin kansu akan rikicin zabar shugabancin majalisar kasa ta 10.
Da yake jawabi ga manema labarai a hedikwatar jam’iyyar a jiya, sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba, ya ce tanade-tanaden majalisun biyu ya jaddada bukatar barin ‘yan majalisar su zabi shugabanninsu da kansu ba tare da tsuma bakin wasu daga wajen majalisar ba.
Da dumi-dumi: Kwankwaso ya bayyana abubuwan da suka tattauna da Shugaba Tinubu
Ya kuma bayyana cewa ‘yancin ‘yan majalisa wani abu ne mai matukar muhimmanci a tsarin dimokuradiyya da kundin tsarin mulki, inda ya kara da cewa ‘yancin majalisa na zabar Shugabannin su tsari ne mai zaman kansa a tsarin dimokuradiyya.
Ya ce tun lokacin da jam’iyyar PDP ta bayyana matsayinta na cewa tana da sha’awar shugabancin majalisar ta 10, ake ta yunkurin tursasawa, muzgunawa da kuma yi wa zababbun ‘yan majalisar barazana da nufin yiwa yunkurin nasu kafar angulu don kar su sami shugabancin majalisar.
Jam’iyyar PDP ta kara da cewa ‘yancin ‘yan majalisa wani sharadi ne a dimokuradiyya wanda indai dimokuradiyya ake so dole baiwa duk dan majalisar damar shiga ya zaba ko a zabe shi a cikin shugabancin majalisar . inji shi.