Daga Sidi Ibrahim Jega
Gwamnan jihar Kebbi Kwamaret Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu ya yi sabbin nade-nade a gwamnatinsa domin taya shi gudanar da aiki tare da samar da ayyukan cigaba ga al’ummar jihar .
Gwamnan yace ya yi nade-naden ne duba da cancantar wadanda aka nada tare da duba tarihin yadda suka gudanar da aikin su a baya.
Hotuna: Yadda Gwamnatin Kano ta rushe shagunan da aka yi a filin idi
Ga Nade Naden kamar haka:
1. Alh. Lawal Labbo Maishanu –Deputy Chief of Staff( Mataimakin Shugaban Ma’aikata)
2. Abubakar Ahmed – Personal Assistant to the Deputy Governor (Mataimaki na Musamman ga Mataimakin Gwamna)
3. Alh. Ibrahim Adamu – Senior Special Assistant on media and publicity (Babban Mataimaki na Musamman akan Yada Labarai da Yada Labarai)
4. Yahaya Salisu Danjada – Special Assistant on new media (Mataimaki na musamman kan sabbin kafafen yada labarai)
5. Tukur Abdullahi – Senior Special Assistant
(Babban Mataimaki na Musamman)
Kadaura24 ta ruwaito cewa, ana sa ran wannan nadin zai taimakawa sabon gwamnan wajen gudanar da aiki sa yadda ya kamata.
Idan ba’a manta ba wannan shi ne karo na biyu da gwamnatin jihar kebbi ta fitar da sunanyen mutanen da ta baiwa mukamai. a baya ma sabon gwamnan jahar kebbi Dr. Nasiru Idris Kauran Gwandu ya nada:
Barrista Attahiru Maccido a matsayin Shugaban ma’aikata.
Alhaji Yakubu Bala Tafidan Yauri a matsayin Sakataren gwamnatin jahar kebbi.
Tare da nada Aminu Musa Danko a matsayin Hadimi na musamman ga maigirma gwamnan jahar kebbi.