Da dumi-dumi: Kwankwaso yayi ganawar sa’o’i hudu da Tinubu a birnin Paris

Date:

Daga Kamal Yahaya Zakaria

Zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya yiwa jam’iyyar NNPP a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, sun yi ganawar akalla sa’o’i hudu a birnin Paris na kasar Faransa a ranar Litinin, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.

 

A tsakiyar tattaunawar, TheCable ta fahimci cewa, akwai yuwuwar shigar Kwankwaso cikin gwamnati mai zuwa yayin da Tinubu ke shirin kafa “gwamnatin hadin kan kasa” – wanda ke nufin bai wa jam’iyyun adawa wasu mukamai a cikin gwamnatin.

Taron ya kuma tattauna batutuwan da suka shafi zaben shugabannin majalisar kasa, gabanin kaddamar da majalisar ta 10 a ranar 13 ga watan Yuni.

Zaben gwamnan kano: Inda aka Kwana game da karar APC da NNPP a Kotu

An fara taron Paris tsakanin Tinubu da Kwankwaso ne da karfe 12:30 na rana kuma aka kammala da karfe 4:45 na yamma, kamar yadda wasu majiyoyi suka shaida wa jaridar TheCable.

Ko Kun zabi aiki ko ba ku zaba ba, mun yi titin Kurna babban layi ne saboda Allah -Ganduje

Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, ya halarci taron yayin da Abdulmumin Jibrin, dan takarar jam’iyyar NNPP kuma tsohon jigo a kwamitin yakin neman zaben Tinubu na daga cikin wadanda suka raka Kwankwaso.

Oluremi Tinubu, Sanata kuma matar zababben shugaban kasa ita ce ta tarbi matar Kwankwaso, Salamatu.

Idan za’a iya tunawa Tinubu da Kwankwaso sun yi aiki a matsayin gwamnonin kano da Lagos a Shekarar 1999 zuwa 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...