Daga Isa Ahmad Getso
Hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya NAHCON, ta bayar da tabbacin maniyata aikin hajjin bana ba za su biya karin kudi ba duk da rikicin dake faruwa a kasar Sudan.
“Kamfanonin jirage na mu na cikin gida bayan tattaunawar da mukai da su a lokuta da dama sun amince da dala $250 a matsayin karin kudin tikitin jirgin domin gudanar da aikin na bana”.
Da dumi-dumi: Akwai yiwuwar za a karawa mahajjatan Najeriya kudin aikin hajjin bana
Shugaban Hukumar ta NAHCON, Alhaji Zikrullah Kulle Hassan ne ya bayyana hakan a Abuja yayin horaswar da aka shirya wa ma’aikatan NAHCON da hukumomin alhazai na jihohi da yan jirgin yawo.
Zikirillah ya ce har yanzu ana neman duk hanyoyin da za a bi don warware wannan lamari wanda zai Saukakawa alhazai Kuma aga ba Wani Alhaji ko Hajiya da ya biya karin wasu kudaden.
Muna fatan komai zai daidai a kasar sudan ta yadda za’a iya amfani da sararin samaniyar Sudan don samun saukin tafiya zuwa kasa mai tsarki.
A cewarsa, kamfanonin jiragen sama – Air Peace, Azman, Max Air da kuma Aero Contractors – ne suka nemi Karin kuɗin Saboda rikicin dake faruwa a kasar Sudan, wanda zai karawa tafiyar tsayi zuwa kasar Saudiyya.
Za a iya cewa kamfanonin jiragen sun ki sanya hannu kan yarjejeniyar jigilar jiragen da NAHCON saboda karin kudin da aka kashe ta hanyar amfani da wata hanya.
Ya kara da cewa hukumar ta su ta sanya ranar 25 ga watan Mayu domin fara jigilar maniyyata zuwa Nigeria zuwa kasa saudiyya.