Mutane 7 Sun Rasa Rayukansu Bayan Sun Sha Wani Shayi A Gidan Biki A Kano

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Kimanin Mutane 7 ne ake fargabar sun mutu tare da kwantar da wasu da dama a asibiti bayan sun sha shayin da ake zargin an yi da wani ganyen garin da aka fi sani da Zakami a wajen wani bikin aure a Kano.

 

Zakami yana ƙunshe da sinadari masu cutarwa ga al’umma.

Shedun gani da ido sun ce lamarin ya shafi kusan mutane 50 kuma har yanzu ba akai ga gano wasun su ba. Lamarin ya faru ne a unguwar Sheka da ke karamar hukumar Kumbotso a cikin birnin Kano.

Da dumi-dumi: Kotun Sauraren Kararrakin Zaɓe ta Kori Koken da aka shigar akan Tinubu

Daya daga cikin wadanda suka shaida lamarin, Sanusi Yahaya, wanda kuma dan uwa ne ga amaryar, ya ce ana zargin shayin an saka wasu magunguna daban-daban bayan wanda aka Saba sakawa a shayi .

Ya ce Shan irin wancan shayi dai ya zama ruwan dare ga matasan yankin musamman masu shaye-shayen miyagun kwayoyi a lokacin bukukuwa, inda suke fakewa da bikin don shan kwaya.

“Sun dafa shayin kuma su da kansu ba su san adadi da nau’in magungunan da ke ciki ba, har wasu daga cikin su suka ki shan shayin . Amma wasu daga cikinsu sun sai suka dage da cewa dole ne su sha shayin, suna masu cewa kwakwalwar su na iya daukar shayin

“Bayan shan shayin, mutane biyu sun mutu, wasu sun murmure yayin da wasu ke kwance a asibiti,” in ji shi.

Wani shaida Abdullahi Muhammad ya ce ya zuwa ranar Talatar da ta gabata mutane bakwai ne suka mutu.

Ya ce wasu daga cikin wadanda ke kwance a asibiti ba ’yan unguwar ba ne amma sun zo wucewa ne kawai suka ana shan shayin suma suka tsaya suka sha.

“Ba mu san ainihin adadin ba a yanzu, amma da safe an tabbatar da mutuwar bakwai. Wasu ma ba a gayyace su zuwa daurin auren ba, sun zo ne domin su yi sha kwaya kawai,” inji shi.

Majiyar Kadaura24 bata samu jin ta bakin angon ba, game da lamarin saboda an ce ya gudu shi da wasu abokansa .

Duk Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ci tura domin ba a same shi a waya ba.

Kuma har lokacin hada wannan rahoton Kiyawan bai amsa sakon da jaridar Daily trust ta aika masa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...