Daga Auwal Alhassan Kademi
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana cewa gwamnan jihar sokoto mai barin gado Alhaji Aminu waziri Tambuwal ne ya lashe zaben Sanatan Sokoto ta kudu.
Baturen zaɓen, Farfesa Abubakar Abdullahi Bagudo ya ce Tambuwal na PDP ya lashe zaɓen da ƙuri’u 100,860.
Har ila yau, abokin karawarsa, wanda shi ne Sanata mai ci ƙarƙashin jam’iyyar APC, Abdullahi Ibrahim Ɗanbaba, ya zo na biyu da ƙuri’u 95,884.
Hakan na nufin Tambuwal ya ci zaɓen da tazarar ƙuri’u 4,976.